Kofin Afrika : Najeriya ta sha da kyar

victor moses
Image caption Victor Moses ya ceto Najeriya

Najeriya ta samu nasarar zuwa matakin gab da na kusa da na karshe na cin kofin kwallon kafa na Afrika bayan da Victor Moses ya jefa kwallaye biyu a ragar Ethiopia wato Habasha ta bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Moses dan shekara 22 wanda ya ke kungiyar Chelsea ya jefa kwallon farko ne a bugun fanareti bayan dan wasan baya na Habasha Alula Girma ya yi masa keta ana saura minti 10 a tashi.

Dan wasan na Najeriya ya sake samun bugun fanareti wanda ya buga kuma ya ci a minti na 90 lokacin da mai tsaron gidan Habasha Sasay Bancha ya kayar da shi aka kuma kori golan daga wasa tare da maye gurbinsa da wani dan wasan.

Da Najeriya ba ta sami nasarar cin kwallayen ba da ta yi asarar zuwa matakin na gaba ga kasar Zambia akan tsarin yawan katin gargadi da aka baiwa 'yan wasanta.

Najeriya ta kammala wasannin rukunin a matsayin ta biyu da maki 5 a wasanni 3, ya yin da Burkina Faso ta zama ta daya a rukunin na uku wato Group C da maki 5 a wasanni 3 amma da bambancin kwallaye 4.

Najeriya za ta kara da Ivory Coast ranar Lahadi 3 ga watan Fabrairu a wasan gab da na kusa da na karshe.

Karin bayani