Kofin Afrika : Zambia ta yi waje

'yan wasan zambia
Image caption 'Yan Zambia ba su yi karko ba a gasar Kofin Afrika

Kasar Zambia dake rike da Kofin kasashen Afrika ta yi waje daga gasar bayan da ta yi canjaras ba bu ci tsakaninta da Burkina Faso wadda ita kuma ta tsallake zuwa mataki na gaba.

'Yan Zambiyan sun shiga wasan ne da maki dai dai da Najeriya a rukuni na uku, Group C, wadda ita kuma ta sami damar tsallake wa zuwa mataki na gaba sakamakon cin Ethiopia da ta yi 2-0.

Wannan shi ne karon farko da wata kasa mai rike da Kofin gasar ta yi waje a matakin wasannin rukuni tun bayan Algeria a 1990 lokacin da ake da rukunai hudu da su ka kunshi kasashe uku-uku.

Wannan shi ne karon farko da Burkina Faso ta sami nasarar zuwa zagaye na biyu na gasar tun lokacin da kasar ta karbi bakunci a 1998.

Karin bayani