A kan Hazard: Chelsea ta yi wa FA korafi

eden hazard
Image caption Eden Hazard ya fusata da mai dauko kwallo a bayan fili

Kungiyar Chelsea ta aika wa Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila, FA, takardar korafi a kan shirin Hukumar na kara hukuncin hana dan wasanta Eden Hazard buga wasa.

Hazard ba zai buga wasanni uku ba saboda korarsa da alkalin wasa ya yi a kan taka mai dauko kwallo a bayan fili da ya yi.

Alkalin wasa ya kori dan wasan ne a karawar Swansea da Chelsea ta wasan kofin kalubale na Capital One zagaye na biyu na wasan kusa da karshe ranar 23 ga watan Janairu.

Dan wasan ya taka mai dauko kwallon ne a bayan fili wanda ya kwanta a kan kwallon lokacin da ya ke fafutukar daukar ta a minti na 78, lokacin a na 0-0, kuma Chelsea na bukatar cin kwallaye biyu.

A kan hakan ya fuskanci hukuncin kauracewa wasanni uku amma hukumar ta FA ta na ganin hukuncin ya yi sauki.

Chelsea kuma na ganin hana dan wasan dan kasar Belgium mai shekaru 22 buga wani karin wasan bayan guda ukun hukuncin ya yi tsanani.

A wannan makon ne klub din zai san ko ya sami nasara a kan korafin kara hukuncin da ya yi.

Daga baya Hazard ya baiwa matashin mai dauko kwallon daga bayan fili, mai suna Charlie Morgan dan shekara 17 hakuri.

Karin bayani