Drogba dan wasanmu ne in ji Shanghai

Drogba
Image caption Drogba ya sabawa kwantaraginsa in ji Shanghai Shenhua

Kungiyar kwallon kafa ta Shanghai Shenhua ta ce kawo yanzu Didier Drogba dan wasanta ne kuma komawarsa kungiyar kwallon kafa ta Galatasaray domin ya taka leda a can ya sabawa ka'idojin kwantaraginsa.

Tsohon shahararren dan wasan na Chelsea ya cimma matsaya da kungiyar game da yarjejeniyar taka leda a klub din na tsawon wa'adin watanni goma sha takwas.

"Lamarin ya ba kungiyar mamaki" a cewar Shenhua, wacce ta kai Drogba China karkashin yarjejeniyar da suka cimma a watan yunin bara .

"Kawo yanzu Drogba dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Shanghai Shenhua ne saboda wa'adin kwantaraginsa bai zo karshe ba".

Kungiyar kwallon kafa ta Galatasaray ta yi shelar cewa Drogba zai soma taka leda a kulob din bayan ya gama yi wa kasarsa hidima a gasar kofin Afrika.

Karin bayani