Hukumar FA ta Ingila ta tuhumi Ferguson

alex ferguson
Image caption Alex Ferguson ya zargi lasiman da nuna wa kungiyarsa bambanci

Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila, FA, ta tuhumi kocin Manchester United Sir Alex Ferguson da laifin sukan mataimakin alkalin wasa a kan aikinsa.

Kocin ya soki lasiman Simon Beck ne a wasansu da Tottenham ranar 20 ga watan Janairu da su ka ta shi kunnen doki 1-1.

Sir Alex ya soki mataimakin alkalin wasan kan yadda yaki baiwa Manchester United jifa da kuma bugun daga kai sai mai tsaron gida da a wasu lokutan wasan da su ke ganin ya kamata ya nuna domin alkalin wasa ya basu amma ya yi kememe ya ki.

Kocin ya ce ''mun tuna shi sosai yadda a wasanmu da Chelsea a 2010 ma lokacin da Didier Drogba ya yi satar gida amma ya ki nuna wa ya kyale shi.''

A kan kalaman na Ferguson Hukumar Kwallon ta Ingila ta ce ya sabawa dokarta ta E3 inda ya ke zargin lasiman din da nuna goyan baya ga wani bangare.

Sir Alex din ya na da dama har zuwa karfe 4 na ranar Juma'a ya kare kansa.

Sai dai daman an ruwaito Kocin na Manchester United kan tuhumar ya na cewa da alamu akwai wata kullalliya tsakanin Hukumar da shi amma ba dai wadannan kalamai da ya yi ba.

Karin bayani