Ivory Coast ta kare kimarta

max gradel
Image caption Max Gradel na Ivory Coast wadda ake gani za ta dauki Kofin Afrika

Ivory Coast, ta daya a rukuni na hudu wato Group D na gasar cin Kofin Afrika ta kare kimarta ta kin bari a yi galaba a kanta a gasar inda ta tashi canjaras 2-2 da Algeria.

Algeria wadda tun kafin karawar ta yau an fidda ita daga gasar ta kasa cin bugun daga kai sai mai tsaron gida da ta samu tun da farko ta hannun Ryad Boudebouz.

Sai dai kuma a minti na 64 Sofiane Feghouli ya yi sa'ar cin bugun fanaretin da Algerian ta sake samu.

A minti na 70 kuma Hilal Soudani ya ci wa Algerian kwallo ta biyu da ka.

Amma kuma can a minti na 77 Didier Drogba ya rama kwallo daya, minti uku tsakani kuma Wilfred Bony ya farke ta biyun.