Beckham zai koma kulob din Faransa

Tsohon kyaftin din Ingila David Beckham
Image caption Tsohon kyaftin din Ingila David Beckham

Ana sa ran daya daga cikin 'yan kwallon kafa da suka yi fice a duniya, kuma dan wasan Ingila David Beckham, zai koma kulob din Paris St German.

Dan wasan mai shekaru 37 a duniya ba shi da kulob tun da ya bar L-A Galaxy ta jihar California a bara.

Rahotanni daga kafafen yada labarai na cewa Beckham zai sanar da komawarsa kulob din, da zarar an kammala duba lafiyarsa.

Masu kudin Qatar ne suka zuba jari a kulob din na Paris St. German a shekarar 2011, kuma kulob din shi ne kan gaba a gasar cin kofin zakarun Faransa.

Beckham tsohon kyaftin din Ingila ya yi fice ne a lokacin da yake kulob din Manchester United, haka kuma yayi wasa a Real Madrid da Milan.