Kofin Afrika : Burkina Faso ta tsallake

'yan wasan burkina faso da togo
Image caption Burkina Faso sau biyu ke nan ta je matakin kusa da na karshe

Kasar Burkina Faso ta samu shiga matakin wasan kusa da na karshe na gasar cin Kofin Kasashen Afrika bayan ta ci Togo 1-0.

Dan wasan Burkina Faso Johnathan Pitroipa ne ya ci kwallon a minti na 105 na karin lokaci bayan an kammala mintuna 90 na wasan ba bu ci a tsakani.

Da wannan nasara Burkina Faso za ta kara da Ghana ranar Laraba 6 ga watan Fabrairun nan, ya yin da Najeriya za ta fafata da Mali a wannan rana.

Tun da farko dai Najeriya ta sami galaba a kan Ivory Coast da ci 1-0 abin da ya bata damar wasan kusa da na karshen da Mali.

Wannan shi ne karo na biyu da Burkina Faso ta tsallake zuwa wasan kusa da na karshe na gasar Kofin Afrika bayan da ta sami irin wannan dama a 1998 lokacin da kasar ta karbi bakuncin gasar.

Karin bayani