Paul Gascoigne na tsaka mai wuya

paul gascoigne
Image caption Paul Gascoigne ya zama dan giya

Tsohon dan wasan kwallon kafa na Ingila Paul Gascoigne yana cikin halin tsaka mai wuya sanadiyyar shan barasa ba kakkautawa da ya ke yi kamar yadda wakilinsa Tery Baker ya bayyana.

Ya yin da dan wasan mai shekara 45 ya ke gabatar da jawabi a wurin wani taron bada tallafin taimakawa mabukata a Northampton ranar Alhamis an ga yana karkarwa kuma maganarsa tana sassarkewa.

Gascoigne wanda ya fito fili ya bayyana cewa yana fama da matsalar shan barasa har ta kai an kai shi gidan kula da masu irin wadannan matsaloli, sau biyu ana adana shi a gidan masu larurar tabin hanakali a 2008.

Wakilin nasa ya ce ''rayuwar dan wasan ko da yaushe tana cikin hadari saboda yana ta'ammali da barasa sosai.

Kuma da alamun babu wanda zai taimaka masa.''

Sai dai kuma Kungiyar Kwararrun 'yan wasa ta Ingila ta ce za ta ci gaba da taimaka masa kamar yadda ta yi a baya.

Shugaban kungiyar Gordon Taylor yana fargabar rayuwar Gascoigne na iya zama kamar ta tsohon dan wasan Manchester United George Best wanda ya mutu a 2005 yana da shekaru 59 bayan ya yi fama da matsalar shan giya.

Paul Gascoigne ya fara ta'ammali da giya a kai a kai tun lokacin da yake wasa bayan aurensa ya mutu da matarsa Sheryl a 1998.