'Yan Ivory Coast na bayan kocinsu

ivorycoast da najeriya
Image caption 'Yan wasan Ivory Coast na son ci gaba da zama tare

Dan wasan baya na kasar Ivory Coast Sol Bamba ya ce takwarorinsa na kungiyar kwallon kafar kasar na nan daram a bayan kocinsu Sabri Lamouchi duk da fitar da su da aka yi a gasar cin Kofin Afrika a wasan gab da na kusa da na karshe.

'yan wasan na Ivory Coast dai su ne masu fashin bakin wasanni ke gani zasu dauki kofin amma Najeriya ta fitar da su da ci 2-1 ranar Lahadi (jiya).

Sol Bamba ya ce '' 'yan wasan suna son kocin ya ci gaba da zama a matsayinsa, amma kuma a Afrika idan ka yi rashin nasara a wasa sai a kori koci, amma dai muna fatan hakan ba zata kasance ba a kansa, zamu saurara mu gani.''

Lamouchi ya kama aiki a matsayin kocin Ivory Coast a watan Mayu bayan an kori Francois Zahoui, duk da cewa tsohon dan wasan na Faransa mai shekara 41 bai taba koyar da wata kungiya ba.

Bayan rade-radin da ake yi game da makomar kocin da dama 'yan kasar na ganin galibin zaratan 'yan kwallon Ivory Coast din da tauraruwarsu ke haskawa a wannan lokacin kamar su Didier Drogba da Didier Zokora sun zo karshen zamaninsu na bugawa kasar wasa.

Sai dai Bamba ya na fatan ayarin zaratan 'yan wasan za su ci gaba da bugawa kasar har zuwa gasar cin Kofin Duniya ta 2014 da za ayi a Brazil.

Ya ce ''wasan kwallon kafa yana tattare da kalubale wata rana kaga fari wata rana rana kuma ka ga baki, idan kayi rashin nasara sai ka koyi darasi ka mike ka ci gaba.'' ya ce muna da wasannin neman zuwa gasar cin Kofin Duniya a don haka muna harin gaba.

Karin bayani