An yi coge a wasannin kwallon kafa 680

Wain Wright na rundunar 'yan sandan nahiyar Turai
Image caption Wain Wright na rundunar 'yan sandan nahiyar Turai

Masu bincike a Birtaniya sun ce, wani wasa da aka buga a Ingila na cikin wasanni 680 da aka yi cogensu a fadin duniya.

'Yan sandan nahiyar Turai ba su fito fili sun bayyana ko wane wasa bane, aka yi cogensa a Ingila ba.

Sai dai 'yan sandan sunce sun gano wasu gungun masu aikata laifuka dake zaune a nahiyar Asia, wandanda ke shirya wasannin.

Wasu jami'an wasa 425 da jami'an kulob-kulob da 'yan wasa da kuma wasu masu aikata laifuka ake zargi da hannu a al'amarin.

Wasannin da aka yi coge

A wani taron manema labarai a birnin Hague, 'yan sandan nahiyar Turai sun yi ikirarin cewa:

Wasan da aka yi cogen nasa a Ingila, an yi shi ne a shekaru uku zuwa hudu da suka wuce.

Ba za a bayyana ko wane wasa bane saboda shari'ar da ake yi.

Wasu wasannin da aka yi zamba a cikinsu sun hada da na gasar cin kofin duniya da na cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Turai.

Haka kuma an samu cogen ne a wasu manyan wasannin league na nahiyar Turai.

A wasannin da aka buga a Jamus kadai, masu aikata manyan laifukan sun wawure fam miliyan 13 da dubu dari takwas kan hada zambar wasanni.

Kuma sun samu ribar fam miliyan shida da dubu dari tara.

A cewar jami'an, wannan somin tabi ne kawai.

Baki daya dai ana zargin anyi zambar wasanni 380 a nahiyar Turai, yayin da wasu taka ledar 300 aka yi cogensu a nahiyar Afrika da Asiya da kuma Kudanci da tsakiyar Amurka.