An karbi Gascoigne a asibitin Amurka

paul gascoigne
Image caption Paul Gascoigne na fama da matsalar shan giya

An karbi tsohon dan wasan Ingila Paul Gascoigne a wani asibitin Amurka domin yi masa magani kan matsalar yawan shan giya.

Gascoigne mai shekaru 45 ya kai kansa da kansa ne asibitin wanda ba a bayyana sunansa ba kamar yadda kamfaninsa ya tabbatar.

Tsohon dan wasan na kungiyoyin Newcastle United da Tottenham da kuma Lazio yana fama da matsalar shan barasa tun lokacin da ya dena buga kwallo.

A ya yin da ya ke jawabi a wani taron bada tallafi ne Gascoigne ya fashe da kuka yana shisshika abin da ya tada hankali tare da jawo hankalin jama'a kan halin da ya ke ciki.

A wata sanarwa da ta fitar kungiyar GamePlan ta bayyana cewa Paul Gascoigne dan giya ne da ya ke fama da matsaloli masu wuya wadanda kwararru ke masa magani.

Sanarwar ta kara da cewa Paul ya ji dadi sosai kan yadda aka raja'a wajen taimaka masa a kwanakinnan.

Gascoigne ya shiga ta'ammali da barasa ne ba kakkautawa tun lokacin da yake wasan kwallon kafa da har ta kai an kwantar da shi a asibiti a 1998 bayan da su ka rabu da matarsa Sheryl.

Karin bayani