Coge: Liverpool tace ba a tuntube ta ba

'Yan wasan Liverpool
Image caption 'Yan wasan Liverpool

Kulob din Liverpool ya ce 'yan sandan tarayyar Turai ba su tuntube shi ba game da bincike kan cogen wasannin kwallon kafa.

Rahotanni na ambato wasan da Liverpool ta doke Debrecen da ci daya da nema, a gasar Champions League a shekarar 2009, a matsayin daya daga cikin wasanni 680 da ake zargin an yi cogensu.

Sai dai kulob din bai nuna alamun ya aikata wani laifi ba.

'Yan sandan tarayyar Turai ba su tuntube mu ba, haka kuma babu wata hukuma da ta tuntubi Liverpool." A cewar maI magana da yawun kulob din.

Tsohon dan wasan gaba na Kulob din, Dirk Kuyt ne, ya samu nasarar zura kwallon a ragar abokan karawarsu na kasar Hungary, a wancan lokaci.

'Yan sandan tarayyar Turai sun kwashe watanni 18 suna bincike, inda a ranar Litinin din data wuce suka ce, suna zargin anyi zambar wasu wasanni ciki har da wadanda aka buga a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya, da na cancantar shiga gasannin zakarun nahiyar Turai.