Burkina Faso ta je wasan karshe

dan wasan burkina faso
Image caption Burkina Faso ta je wasan karshe a karon farko

Burkina Faso za ta kara da Najeriya a wasan karshe na gasar cin Kofin Kasashen Afrika da ake yi a Afrika ta Kudu.

Burkina Faso ta sami wannan dama ne a karon farko a tarihinta bayan ta fitar da Ghana a bugun fanareti bayan sun tashi wasan 1-1.

A bugun fanaretin Burkina Fason ta ci kwallaye 3 Ghanan kuma ta ci 2.

A ranar Lahadi ne 10 ga watan Fabrairu za a yi karawar karshen tsakanin Najeriya wadda tun da farko ta fitar da Mali da ci 4-1 da Burkina Fason.