FIFA ta bullo da intanet don cogen wasa

sepp blatter
Image caption Blatter ya yi gargadi kan cogen wasa

Hukumar kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta bullo da hanyar amfani da intanet ta yadda za a rinka bayar da rahoton cogen wasa da sauran laifukan saba wa dokokinta.

Ta wannan tsari jama'a za su iya bada rahoton wani abu da su ke gani ya saba wa ka'idojin Hukumar Wasannin.

Ranar Litinin ne wani rahoton Hukumar 'yan sandan Turai, Europol, ya bayyana cewa an yi cogen wasanni 680 wadanda su ka hada da wani a Ingila ta yadda aka tsara yadda sakamakonsu zai kasance.

A shekarar da ta wuce shugaban FIFA, Sepp Blatter ya yi gargadin cewa coge na barazanar zubar da kima da martabar wasan kwallon kafa.

A 2011 Hukumar ta sanar da wani shiri da za ta kashe fam miliyan 17.5 da za ta rinka bin diddigin cogen wasa da cacar wasanni wadda ba ta ka'ida ba tare da hadin guiwar hukumar 'yan sanda ta duniya.

Karin bayani