Kofin Afrika: An dakatar da alkalin wasa

caf
Image caption CAF za ta duba hukuncin Pitroipa

Hukumar Kwallon Kafa ta Afrika, CAF, ta dakatar da lafrin da ya yi alkalancin wasan kusa da na karshe tsakanin Burkina Faso da Ghana ranar Laraba.

Hukumar ta yi wannan hukunci a kan Slim Jdidi ne dan kasar Tunisia saboda yadda ya yi alkalanci wasan ta yadda wasu abubuwan da ya yi ba su da ce ba .

Burkina Fason dai ta daukaka kara a kan hukuncin korar dan wasanta Jonathan Pitroipa da lafrin ya yi da hakan zai sa ba zai samu damar buga karawar karshe da za ta yi ba da Najeriya.

Burkina Fason ta na son Hukumar ta CAF ta soke wannan hukunci ta dawo da dan wasan.

Sai dai kuma Hukumar ta ce hakan za ta yuwu ne idan alkalin wasan a rahotonsa da zai gabatar na wasan ya amince cewa kuskure ya yi na korar Pitroipa.

Amma kuma babban sakataren hukumar ta CAF Hicham El Amrani ya ce ranar Juma'a za su tattauna batun na Pitroipa.

Karin bayani