Jamie Carragher zai yi ritaya

jamie carragher
Image caption Jamie Carragher ya shiga Liverpool tun ya na shekara 9

Dan wasan baya na kungiyar Liverpool Jamie Carragher zai yi ritaya daga wasann kwallon kafa a karshen kakar wasanni ta bana.

Dan wasan mai shekaru 35 sau 700 ya na bugawa Liverpool wasa a matakin manya kuma Ian Callaghan ne kawai ya fi shi yi wa kungiyar wasa a tarihin 'yan wasanta.

Tun yana dan shekara tara ne Carragher ya shiga Liverpool ta matasa kuma ya fara buga mata wasa a karawarta da Middlesbrough a watan Janairu na 1997.

Yana daga cikin 'yan klub din lokacin da su ka dauki Kofin Uefa a 2001 da Kofin Zakarun Turai a 2005 da Kofunan Kalubale na Ingila FA biyu da kuma kofunan Lig na Ingila uku.

Haka kuma sau 38 Jamie Carragher ya bugawa Ingila wasa.

Karin bayani