Chile Open : Nadal ya yi nasara

rafeal nadal
Image caption Rafeal Nadal ya fara samun kansa

Tsohon zakaran dan wasan tennis na duniya Rafeal Nadal ya fara samun kansa bayan ya yi fama da ciwon ciki da guiwa tsawon watanni takwas.

A gasar Chile Open Nadal ya yi nasara a kan Federico Delbonis dan kasar Argentina da maki 6-3 6-2.

Da wannan nasara yanzu ya tsallake zuwa zagaye na uku na gasar.

A ranar Alhamis ne kuma Nadal din zai yi wasansa na gaba, na mutane bibbiyu, tare da Juan Monaco dan Argentina da gamayyar Guillame Rufin da Flippo Volandri.

Rafeal Nadal bai je gasar wasan Olympics ta Landan ta 2012 da gasar US Open da kuma ta Australian Open ba saboda rashin lafiya.

Dan shekara 26 Nadal yanzu shi ne na biyar a gwanayen tennis na duniya.

Karin bayani