Kofin Afirka: Wanene zai daga shi?

Sabon Kofin Kwallon Kafa na Kasashen Afirka
Image caption Saura kiris a san wanda zai daga Sabon Kofin Kwallon Kafa na Kasashen Afirka

Nan gaba a yau Lahadi ne za a karkare Gasar Kwallon Kafa ta cin Kofin Kasashen Afirka, lokacin da zakarar gasar har sau biyu, wato Najeriya, za ta kara da Burkina Faso, wacce nasararta ta ba-da mamaki a gasar.

A farkon gasar dai Najeriya ta dan yi nauyin jiki amma a sauran wasanninta ta farfado.

Ita kuwa Burkina Faso masharhanta ta baiwa mamaki da salon taka ledarta, kasancewa sau daya ta taba wuce matakin farko a gasar.

A wasan neman matsayi na uku kuwa, ranar Asabar Mali ce ta ci gari bayan da ta lallasa Ghana da ci uku da daya.

Karin bayani