Nigeria ce zakarar Afrika ta 2013

Latsa nan domin ganin sabbin bayanai

Nigeria ta doke Burkina Faso da ci 1-0, abinda ya bata damar kasancewa zakarar kwallon kasashen Afrika ta 2013.

20:42:Kyaftin din Nigeria Joseph Yobo ya daga kofi inda 'yan wasanta suke ta rawa suna murna, shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma ne ya mika musu kofi.

20:39: 'Yan wasan Nigeria sun hau dandamali suna karbar kyaututtukansu - yayin da shugaban Afrika ta KuduJacob Zuma yake samu lambobi a wuya, shi kuma shugaban Majalisar Dattawan Nigeria David Mark ke rungume su.

20:37: 'Yan wasan Burkina Faso na karbar lambobin yabonsu bayan sun kasance na biyu: Babu shakka sun taka rawar gani a wannan gasa ta bana.

2032: Yan wasan Nigeria na zagaya fili da tutar kasarsu domin murna - sannan suna daga koci Stephen Keshi, yayin da 'yan Burkina Faso ke kuka.

20:32: A sakon da ya aiko mana ta shafinmu na BBC Hausa FacebookTanko Katuka Kagarko cewa yayi: "Muna jira a filin jirgin sama domin tarbanku 'yan wasan Nigeria".

22:26: Baba Yakubu Makeri mai yiwa BBC sharhi a Afrika ta Kudu: Kocin Nigeria Stephen Keshi ya kafa tarihi bayan da ya lashe wannan gasa a matsayin koci a shekara ta 1994, a yanzu gashi ya sake lashe wa a matsayin koci. Burkina Faso basu tayar da hankalin Nigeria sosai ba amma dai sun yi kokari matuka idan aka kalli gasar baki daya.

22:23: ZAKARUN KWALLON AFRIKA NA SHEKARA TA 2013 - NIGERIA

20:22: Alkalin wasa ya hura tashi: Nigeria ta doke Burkina Faso da ci 1-0.

20:18: An shiga karin lokaci. Nigeria 1-0 Burkina Faso

20:16: An cire Sunday Mba wanda ya zira kwallon Nigeria, inda aka sako tsohon dan wasan baya na Everton Joseph Yobo.

20:14: Saura kiris, sau biyu Nigeria na zubar da damarmaki masu kyau. Victor Moses da Brown Ideye ne suka baras da wadannan damarmakin.

20:13: Paul Koulibaly na Burkina Faso ya shigo inda ya maye gurbin Moumouni Dagano wanda ya fi kowa zira kwallo a Burkina Faso.

20:10: Wakilin BBC Aliyu Abdullahi Tanko a Afrika ta Kudu: Ya kamata Nigeria ta rinka amfani da damarta domin Burkina Faso za su iya samun dama a kowanne lokaci. Saboda a wasan farko da kasashen biyu suka buga a rukunin gasar ta bana an tashi ne 1-1 inda Burkina Faso ta rama kwallonta a mintin karshe.

20:04: Saura mintina 15 a tashi Nigeria 1-0 Burkina Faso.

20:01: Ahmed Musa ya fadi shi kadai a yadi na sha takwas na Burkina Faso, daga nan ne kuma suka ja kwallo inda suka kai mummunan hari - sai dai alkalin wasa ya ce 'yan Burkina sun yi satar gida.

20:00: Burkina Faso sun samu kwana uku ajere.

19:58:Juwon Oshaniwa ya samu katin gargadi saboda ya tade Prejuce Nakoulma. Bugun tazara ga Burkina Faso - amma kwallon bata yi hadari ga Nigeria ba.

19:52: Burkina Faso ta cire Florent Rouamba inda aka maye gurbinsa da Wilfried Sanou.

19:51: Nigeria ta saka Juwon Oshaniwainda ya cire Elderson Echiejile sakamakon raunin da samu. Har yanzu wasa Nigeria 1-0 Burkina Faso.

19:50: A cewar tsohon dan wasan Orlando Pirates Lutz Pfannenstie a BBC radio 5Live Extra, Nigeria na koma wa baya inda suke jiran sai Burkina Faso sun yi kuskure sannan su kai hari.

19:49: Burkina Faso ta samu bugun tazara bayan da aka tade Jonathan Pitroipa, amma bugun baiyi kyau ba.

19:48: Daga dukkan alamu Burkian Faso basu karaya da wannan wasa ba, har yanzu suna kai kora domin rama kwallon da aka zira musu.

19:45: Jonathan Pitroipa ya samu 'yar matsala bayan da 'yan Nigeria suka tade shi, kuma an bayar da katin gargadi ga dan Nigeria John Obi Mikel.

19:42:Saura kiris: Victor Moses ya zubar da dama mai kyawun gaske, daga shi sai gola amma sai ya so kansa mai makon ya bawa Ahmed Musa.

19:41: Ahmed Musa ya shigo ya karbi Uche

19:36:Brown Ideye ya zubar da dama mai kyau wacce da ta baiwa Nigeria damar zura kwallo ta biyu. Kwallo ya samu ta gefe wacce ya kwararota amma saura kiris - sai ta fita ta gefen turke.

19:31: An dawo hutun rabin lokaci. Nigeria 1-0 Burkina Faso

19:26: Ya kamata kocin Nigeria Stephen Keshi ya cire daya daga cikin 'yan wasansa na gaba domin ya saka Ahmed Musa, a cewar mai yiwa BBC sharhi kan wasanni Malam Sheshu Lawal.

19:24:Nigeria 1-0 Burkina Faso: Kada ku manta za ku iya shiga cikin shirin ta hanyar aiko mana da sakonninku ta BBC Hausa Facebook ko kuma ta Twitter @bbchausa ta hanyar amfani da #bbcafcon

19:18:Hutun rabin lokaci: Kwallon da Sunday Mba ya zira ce ta baiwa Nigeria galaba da ci 1-0 kan Burkina Faso. A yanzu an tafi asha ruwa a huta.

19:10: Kwallo mai ban sha'awa da Sunday Mba ya zira. Victor Moses ne ya fara doka kwallon amma sai 'yan bayan Burkina suka tare. Daga nan sai kwallon ta koma wurin dan wasan na Enugu Rangers wanda ya zira ta a raga ba tare da wata matsala ba.

19:10: Kwaloooooo Nigeria 1-0 Burkina Faso Sunday Mba

19:03: An baiwa Florent Rouamba na Burkina katin gargadi saboda ya tade Victor Moses

19:03:Mintina 33 da fara wannan wasa amma har yanzu kasashen biyu na kokarin samun kwallon farko. Nigeria 0-0 Burkina Faso.

18:56: Burkina Faso sun samu bugun tazara daga wuri mai hadari kusan yadi na 25 amma Augsburg ya buga kwallon waje.

Image caption Wasa ya dau zafi kowa na kokarin neman nasara

18:55: Kawo yanzu dai golan Burkina Faso Daouda Diakite ne yafi shiga hadari kan na Nigeria Vincent Enyeama.

18:49: Nigeria 0-0 Burkina Faso:Yakubu Makere, mai sharhi na BBC Hausa a Afrika ta Kudu: Nigeria za su iya yin da-na-sanin damarmakin da suke zubarwa ganin cewa wannan wasan karshe ne.

18:42:Jonathan Pitroipa ya kai kora amma ta fita corner farko ga Burkina Faso - wacce kuma bata yi wata barazana ga 'yan Najeriya ba.

18:49: A sakon da ya aiko mana ta TwitterUbaidullah Muhammad cewa yayi: Up Super Eagles da yardar Allah namu ne Nigeria @bbchausa

18:42: Kada ku manta za ku iya shiga cikin shirin ta hanyar aiko mana da sakonninku ta BBC Hausa Facebook ko kuma ta Twitter @bbchausa ta hanyar amfani da #bbcafcon

18:40: Brown Ideye na Nigeria ya yi kokarin zira kwallo a raga amma alkalin wasa ya ce ya ture mai tsaron gida na Burkina Faso.

18:38:Najeriya ta yi kokarin kai hari amma alkalin wasa ya riga ya ce sun yi satar gida sakamakon bugun tazarar da Victor Moses ya yi.

18:36: Najeriya ta samu kwanar farko

Image caption Filin wasa ya cika makil

1833:

1832: Ciniki ya shiga, har Nigeria ta kai harin farko.

18:30: A sakon da ya aiko mana ta Twitter: Salisu Nura cewa yayi fatan alheri ga tawagar Super Eagles kan wasa da za su buga yau.

18:26: 'Yan wasa sun fito fili inda ake rera taken kasashen biyu. Wakilin BBC Aliyu Abdullahi Tanko ya ce filin ya cika makil.

18:22: A bangaren Nigeria, shugaban Majalisar Dattijan kasar David Mark, na halartar wasan domin karfafawa 'yan Super Eagles gwiwa inda yake wakiltar shugaba Goodluck Jonathan.

18:20: Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Sepp Blatter, na kasar Afrika ta Kudu domin kallon wannan wasa.

18:12: Tawagar Burkina Faso: Diakite, Koffi, B.Kone, Koulibally, Panandetiguiri, D.Kone, Rouamba, Kabore, Pitroipa, Nakoulma, Bance

18:10: Tawagar da za ta bugawa Najeriya, babu Emmanuel Eminike amma akwai Victor Moses: Enyeama, Ambrose, Echielije, Oboabona, Omeruo, Mikel Obi, Mba, Onazi, Moses, Ideye, Uche

Za ku iya shiga cikin shirin ta hanyar aiko mana da sakonninku ta BBC Hausa Facebook ko kuma ta Twitter @bbchausa ta hanyar amfani da #bbcafcon

18:00: Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye yadda wasan karshe ke gudana tsakanin Najeriya da Burkina Faso a gasar cin kofin kasashen Afrika.