CAF 2013: Najeriya da Burkina Faso

Sabon Kofin Kwallon Kafa na Kasashen Afirka
Image caption Saura kiris a san wanda zai daga Sabon Kofin Kwallon Kafa na Kasashen Afirka

Inda za a fafata: Filin wasa FNB, Soccer City Johannesbur: Lahadi 10 Fabreru: Lokaci 18:30 GMT

Sharhi kai tsaye a shashin Hausa na BBC ta rediyo da kuma bbchausa.com/mobile da kuma shashin Turanci na BBC Sport.

Nan gaba a ranar Lahadi ne za a karkare gasar Kwallon Kafa ta cin Kofin Kasashen Afirka, lokacin da Najeriya za ta kara da Burkina Faso, wacce nasararta ta ba-da mamaki a gasar.

A farkon gasar dai Najeriya ta dan yi nauyin jiki amma a sauran wasanninta ta farfado.

Ita kuwa Burkina Faso masharhanta ta baiwa mamaki da salon taka ledarta, kasancewa sau daya ta taba wuce matakin farko a gasar.

A wasan neman matsayi na uku kuwa, ranar Asabar Mali ce ta ci gari bayan da ta lallasa Ghana da ci uku da daya.

Karin bayani