Manchester United ta kara bada rata

ryan giggs
Image caption Ryan Giggs lokacin da ya ci Everton

Kungiyar Manchester United ta kara bada rata a gasar Premier da maki 12 sakamakon nasarar da ta samu a kan Kungiyar Everton da ci 2-0 a Old Trafford.

Da wannan rata da United din ta baiwa mai hamayya da ita Manchester City ta biyu a gasar ta Premier ta na kan hanyar daukan Kofin Premier karo na 20.

Ryan Giggs ne ya fara ci wa Manchester United din kwallon farko a minti na 13 a kakar wasanni ta 23 da ya ke buga wasa.

A minti na 45 ne kuma dab da tafiya hutun rabin lokaci Robin Van Persie ya jefa kwallo ta biyu a ragar 'yan Everton wanda shi kuma kwallonsa ta 23 ke nan a bana.

Wannan dai shi ne karo na hudu da ita kuma Kungiyar Everton ta yi rashin nasara a kakar wasanni ta bana.

Karin bayani