Aston Villa ta fita daga hadari

aston villa
Image caption Aston Villa ta sami nasara ta uku a gida

Kokarin da Kungiyar Aston Villa ta ke yi na ci gaba da zama a gasar Premier ya sami tagomashi sosai da nasarar da ta samu a kan West Ham 2-1.

Yanzu ta fice daga cikin jerin kungiyoyi uku da ke cikin hadarin faduwa daga gasar ta Premier.

Christian Benteke ne a minti na 74 ya fara jefa kwallo a ragar West Ham da bugun fanareti.

Minti hudu a tsakani sai N'zogbia ya kara kwallo ta biyu kafin a minti na 87 kuma Ashley Westwood ya ci kansu da kansu.

Wannan ita ce nasara ta uku da Aston Villa ta samu a gidanta a tsawon kakar wasanni ta bana.

Karin bayani