Balotelli : An ci tarar Inter Milan

mario balotelli
Image caption Mario Balotelli ya sake fuskantar wariyar launin fata

An ci tarar kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan fam 12,900 saboda magoya bayanta sun rinka rera wakokin nuna wariyar launin fata a kan dan wasan AC Milan Mario Balotelli a ya yin karawar Inter Milan din da Chievo.

Balotelli wanda tsohon dan wasan Inter Milan ne ya koma AC Milan daga Manchester City a watan da ya wuce.

Shugaban kungiyar ta Inter Milan Massimo Morati ya nuna nadamarsa a kan halayyar magoya bayan nasu.

Ya kuma yi fatan hakan ba zai sake faruwa ba idan kungiyoyin biyu abokanan hamayyar juna su ka hadu a San Siro ranar 24 ga watan Fabrairun nan.

An ci tarar Juventus ma euro 15, 000 bayan magoya bayan klub din sun rera wakokin nuna bangaranci a kan abokanan hamayyarsu Napoli.

Karin bayani