Buffon: Ba mu damu da 'yan Celtic ba

gianluigi buffon
Image caption Gianluigi Buffon ''ba ma fargabar magoya bayan Celtic''

Mai tsaron gidan kungiyar wasan kwallon kafa ta Juventus ta Italiya Gianluigi Buffon ya ce ba su damu da magoya bayan kungiyar Celtic ta Scotland ba.

Buffon ya na magana ne kan irin damar da 'yan Celtic din za su samu ta magoya bayansu a ya yin karawar da za su yi ta cin kofin Zakarun Turai ran Talatar nan a Glasgow.

Mai tsaron gidan na Juventus dan shekara 35 ya ce ''ba shakka yanayin na Burtaniya ne amma a iya sanina ba bu wani mai goyon bayan wata kungiya da ya taba cin kwallo.''

Ya ce '' ba shakka magoya bayansu za su taimaka musu amma zuwa wani mataki kawai.''

Magoya bayan na Celtic da su ka cika filin wasan Celtic Park a lokacin karawar kungiyar da Barcelona a wasan rukuni na Kofin Zakarun Turai inda ta ci Barcelona sun rinka ihu da rera wakokin kungiyar tasu da hakan ake ganin ya taimaka wa Celtic.