'Yan wasan Super Eagles sun isa Najeriya

Tawagar Najeriya na murnan nasarar cin kofin Afrika
Image caption Tawagar kwallon kafa ta Najeriya na murnan nasarar cin kofin Afrika

Tawagar 'yan wasan kwallon kafa na Najeriya da ta lashe gasar cin kofin kasashen Afrika ta 2013 a Afrika ta Kudu sun sauka a filin saukar jiragen sama na Abuja.

Dandazon mutane ne da suka hada jami'an gwamnati suka taru a filin saukar jiragen sama na Ndamdi Azikwe da ke Abuja domin tarbar su.

Nan gaba a ranar Talata ne shugaban kasar GoodLuck Jonathan, zai shirya wa masu rike da kambun na nahiyar Afrika, liyafar cin abinci ta mussaman a fadar gwamnati.

A waje daya kuma, manajan kungiyar, Steven Keshi ya jaddada cewa bashi da niyyar yin murabus daga mukaminsa.

A wata sanarwa da ya aike wa BBC, Keshi yace sun warware matsalar dake tsakaninsa da hukumar kwallon kafa ta kasar, NFF.

Bayan daukar kofin nahiyar Afrika, abu na gaba da kungiyar Super Eagles ta sa a gaba shi ne, lashe gasar zakarun kwallon kafa na nahiyoyi, a cewar Keshi.