Zakarun Turai : Juventus ta casa Celtic

'yan wasan juventus da celtic
Image caption Juventus ta casa Celtic a Glasgow

Juventus ta lallasa Celtic a gasar cin kofin Zakarun Turai zagayen kungiyoyi 16 karawar farko da ci 3-0 a gidan Celtic wato Celtic Park dake Glasgow.

Alessandro Matri ne ya fara jefawa Juventus kwallonta ta farko a minti uku da fara wasa.

Saura minti goma sha biyar a tashi daga wasan Claudio Marchisio ya ci kwallo ta biyu.

A minti na tamanin da uku ne kuma Mirko Vucinic ya jefa kwallo ta uku a ragar Celtic.

A watan Maris ne za a yi karawa ta biyu a gidan Juventus a Italiya.