Kungiyar Super Eagles za ta iso Najeriya

Tawagar Najeriya na murnan nasarar cin kofin Afrika
Image caption Tawagar kwallon kafa ta Najeriya na murnan nasarar cin kofin Afrika

A ranar Talata ne a ke sa ran tawagar 'yan wasan kwallon kafa na Najeriya, za ta dawo gida, bayan kammala gasar cin kofin zakaru na nahiyar Afrika da aka yi a Afrika ta Kudu.

Ana sa ran tawagar ta Super Eagles zata isa Abuja a ranar Talata, inda ake sa ran ministan babban birnin Najeriyar, Bala Muhammed ne zai karbi tawagar a filin saukar jiragen sama na Nnamdi Azikwe.

Haka kuma da maraicen wannan ranar ce, shugaban kasar GoodLuck Jonathan, zai shirya wa masu rike da kambun nahiyar Afrikan, liyafar cin abinci ta mussaman a fadar gwamnati.

A waje daya kuma, manajan kungiyar, Steven Keshi ya jaddada cewa bashi da niyyar yin murabus daga mukaminsa.

A wata sanarwa da ya aike wa BBC, Keshi yace sun warware matsalar dake tsakaninsa da hukumar kwallon kafa ta kasar, NFF.

Bayan daukar kofin nahiyar Afrika, abu na gaba da kungiyar Super Eagles ta sa a gaba shi ne, lashe gasar zakarun kwallon kafa na nahiyoyi, a cewar Keshi.