Ferguson ya shirya wa Karon batta

alex ferguson
Image caption Alex Ferguson ba ya fargabar haduwa da Madrid

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce ya shirya wa karawar da kungiyarsa za ta yi da Real Madrid ta kungiyoyi 16 zagayen farko.

Ya ce ba shi da wani shakku a karon battar sai dai bai so su ka hadu da Real Madrid a wannan matakin ba.

Ferguson ya ce ya so a ce sun kara ne a wasan karshe da za a yi a Wembley a watan Mayu.

Kocin na Manchester United ya na son samun kyakkyawan sakamako a karawar ta Madrid ta yadda zai fuskanci fafatawar ta biyu a Old Trafford da kwarin guiwa a cikin makwanni uku.

Karin bayani