Matsayin FIFA : Najeriya ta ci gaba

'yan wasan najeriya
Image caption Najeriya ta ci gaba a matsayin FIFA

Najeriya ta yi tashin gwauron zabo a jerin gwanayen Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA , inda ta tsallake mataki 22 ta zama ta 30 a duniya.

Kasar ta samu tagomashin ne sakamakon nasarar da ta samu ta daukar Kofin Kasashen Afrika bayan ta yi galaba a kan Burkina Faso da ci 1-0.

Wannan shi ne mataki na kusa kusa da Najeriyar ta samu a cikin shekaru uku.

Burkina Faso wadda ta fafata da Najeriyar a wasan karshe na Kofin Afrikan ta zama ta 55 a duniya.

Ivory Coast wadda Najeriyar ta fitar a wasan gab da na kusa da karshe ta ci gaba da kasancewa ta daya a Afrika a matsayi na 12 na duniya, Ghana ta biyu a Afrika na bi mata a matsayi na 19 a duniya.

Cape Verde wadda ta kai wasan gab da na kusa da karshe na kofin Afrika a zuwanta na farko ta samu matsayi na 63 daga matsayi na 76.

Kasar Spain ta ci gaba da zama a matsayinta, ta daya a duniya, Jamus na bi mata sai kuma Argentina.

Ingila wadda a da ta ke a matsayi na shida ta cira zuwa matsayi na hudu sakamakon nasarar da ta samu a kan Brazil 2-1 a wasan sada zumuntar da su ka yi a makon da ya wuce.

Ita kuwa Brazil wadda ta dauki Kofin Duniya sau biyar kuma mai masaukin bakin gasar Kofin Duniyar ta 2014 ta na ta 18, matsayi na kasa da ta taba samu, sabo da rashin nasarar da ta yi a wasanta da Ingilan.