Kofin FA : Man City ta casa Leeds

manchester city
Image caption Manchester City ta lallasa Leeds

Manchester City ta samu nasarar zuwa matakin wasan gab da na kusa da karshe na cin Kofin Hukumar kwallon Kafa ta Ingila, FA, bayan ta casa Leeds 4-0.

Kofin na FA dai yanzu shi ne Manchester City ta sa a gaba ganin cewa maki 12 ne tsakaninta da Manchester United da ke kan gaba a Premier.

Yaya Toure ne ya fara jefa kwallo a ragar Leeds a na minti 5 kacal da fara wasa, kafin wasu mintuna 10 kuma Sergio Aguero ya biyo baya da ta biyu da bugun fanareti.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci kuma sai Carlos Tevez ya kara ta uku a minti na 52.

Daga nan ne kuma sai Aguero ya kawo karshen duk wani fata da 'yan Leeds din su ke da shi na yin wani katabus inda ya sake cin kwallo ta 4 a minti na 74.

Leeds ta fitar da Tottenham ce a gasar ta cin Kofin na FA ta zo wannan mataki amma kuma ta kasa tabuka wani abun a zo a gani a wannan karawa.

Karin bayani