Wigan ta yi bajintar shekara 26

wigan huddersfield
Image caption Wigan ta yi bajinta bayan shekaru 24

Callum Mcmanaman ya taimakawa kungiyar Wigan ta kai wasan gab da na kusa da karshe na cin Kofin FA a karon farko bayan shekara 26.

Klub din na Wigan ya yi wannan bajinta ne sakamakon nasarar da 'yan wasansa su ka samu ta buge Huddersfield da ci 4-1.

Mcmanaman ne ya bude cin bayan mintina 31 da fara wasa kafin minti 9 kuma tsakani Arouna kone ya ci ta biyu.

James McArthur ya ci wa Wigan kwallo ta uku a minti na 56, Lee Novak ya baiwa 'yan Huddersfield din kwarin guiwa lokacin da ya jefa musu kwallo daya.

Sai dai kuma hakan ba ta dore ba bayan da Arouna Kone ya karya lagon 'yan Huddersfield din da kwallonsa ta biyu kuma ta hudu ta Wigan din minti daya kafin a tashi.