Kofin FA : Man U ta tsallake gaba

nani
Image caption Nani ne ya fara bude wa Manchester United ci

Manchester United ta samu nasarar zuwa matakin wasan gab da na kusa da karshe na cin Kofin kalubale na Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila FA bayan ta yi galaba a kan Reading 2-1.

Nani ne ya ci wa United din kwallon farko a minti na 69 bayan ya yi canjin Phil Jones wanda aka raunata.

Ba a jima ba kuma a minti na 72 Nani din ya aikawa Hernandez wata kwallo wadda shi kuma ya jefata a raga da ka.

'Yan Reading wadanda dama su ke wasan da zafi zafi ba su karaya ba duk da cin su kwallaye biyu.

Jobi McAnuff ya rama musu kwallo daya a minti na 81.

Yanzu United za ta jira ta ga yadda wasa zai kasance tsakanin Middlesbrough da Chelsea domin sanin kungiyar da za ta fafata da ita a gaba.

Karin bayani