Zakarun Turai : Arsenal ta sha kashi

arsenal Bayern munich
Image caption Arsenal na tsaka mai wuya

Kungiyar Arsenal ta sha kashi a gidanta a hannun Bayern Munich ta Jamus da ci 3 -1.

Wannan ita ce karawar farko ta kungiyoyi 16 da za a fitar da 8 da zasu yi wasan gab da na kusa da karshe bayan karawa ta biyu.

Minti bakwai da fara wasan ne Toni Kroos ya daddage ya sheko wata kwallo wadda ba ta zame a ko ina ba sai cikin ragar Arsenal can kuma a minti na 21 Thomas Mueller ya biyo baya da kwallo ta biyu.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne kuma a dai-dai minti na 55 Lukas Podolski ya rama wa Arsenal kwallo daya wadda ya ci da ka.

Sai dai kuma can a Minti na 77 Mario Mandzukic ya jefa kwallo ta uku ragar Arsenal. Da wannan sakamako Arsenal na da jan aiki a gabanta a karawa ta biyu a Jamus in har tana son zuwa matakin wasan gab da na kusa da karshe ta yin galaba a kan Bayern Munich.

A daya wasan na kofin na Zakarun Turai FC Porto ta Portugal ta yi nasara a kan Malaga ta Spain da ci 1-0.

Joao Moutinho ne ya jefa kwallon a ragar bakin a minti na 56 a wasan da 'yan porton suka mamaye Malagan.

Wannan sakamakon dai ya karya lagon kungiyar ta Malaga wadda ba a yi nasara a kansu ba a wasannin da suke yi na gasar kofin Zakarun Turan.

Porto ma ba ta taba rashin nasara a gidanta ba a gasar Zakarun Turan tun 2009 lokacin da Chelsea ta ziyarce su.