Man U ta damu game da raunin Jones

Phil Jones
Image caption Manchester United ta doke Readingds da ci 2 da 1

Dan wasan kulon din Manchester United Phil Jones, na jiran a tantance girman raunin da ya samu a agararsa, a lokacin karwarsu da Readings.

Dan wasan mai shekaru 20 ya dogara sanda ne, a lokacin da ya bar filin wasa na Old Trafford.

Manajan United ya ce mai yiwuwa Jones ba zai samu taka ledar da za su yi ranar Asabar mai zuwa tare da Queens Park Rangers ba.

"Za mu duba girman raunin ranar Talata." Inji Ferguson.

Sir, Alex na fatan dan wasan bayan, kuma tsohon dana wasan kulob din Blackburn, zai samu lafiya ya shiga karawar da Manchester za ta yi a zagaye na biyu, a Old Trafford ranar 5 ga watan Maris.

Karin bayani