Pistorious ya ce ya dauka dan fashi ya harba

oscar pistorious
Image caption Oscar Pistorious, da wuya ya samu beli

Kotun da ke sauraron belin da zakaran tseren nakasassu na Afrika ta Kudu ke nema, ta yanke hukuncin cewa za ta saurari batun kisan budurwarsa a matsayin lamarin da aka yi da gangan.

Mr Oscar Pistorius ya yi kuka sannan ya sunkuyar da kansa a lokacin da ya ji hukuncin wanda zai sa da wuya ya samu beli.

A wani jawabi da lauyansa ya karanta, Mr Pistorius ya ce ya harbe budurwar tasa ne Reeva Steenkamp bisa kuskure - yana zaton cewa wani dan fashi ne .

Ya kara da cewa hankalinsa ya tashi matuka lokacin da ya fahimci cewa bata kan gadonsa.

Da yake magana a lokacin addu'o'i ga marigayiyar, dan uwanta Mike Steenkamp -- ya ce suna mayar da hankali kan abubuwan alherin da ta yi ga rayuwar mutane