Robson : Wenger ne ya hana Arsenal kofi

arsene wenger
Image caption Arsene Wenger rabonsa da kofi shekaru 8

Tsohon dan wasan tsakiya na Arsenal Stewart Robson ya ce kocin klub din Arsene wenger shi ne ya sa kungiyar ta kasa daukar kofi ko da guda daya a shekaru 8.

Robson ya soki lamirin Wenger da cewa ba ya tabuka wani abun-a-zo-a-gani a aikinsa.

kuma ya ce kociya ne da ba shi da wata dabara da ya kamata a kore shi tun shekaru biyar da suka wuce.

Arsenal din a Talatar nan ta ke wasa da Bayern Munich a gasar cin Kofin Zakarun Turai.

Wannan gasar ita kadai ce ta rage wa Arsenal a saran daukar wani kofi a bana, saboda tuni daman aka fitar da ita daga wasannin kofin FA da na Capital One kuma ita ce ta biyar a gasar Premier ta Ingila.