Arsene Wenger na nan daram a Arnenal

arsene wenger
Image caption Arsene Wenger zai iya sabunta zamansa a Arsenal

Kocin Arsenal dake tsaka mai wuya kan ci gaba da kasance wa a kungiyar Arsene Wenger zai ci gaba da zama ko da kuwa klub din bai samu damar shiga gasar Kofin Zakarun Turai ta gaba ba.

Akwai alamun cewa kungiyar ba ta da niyyar korar kociyan ko da bai kai ta ga gasar ba ta kakar wasanni mai zuwa.

Har yanzu mutumin da ya fi yawan hannun jari a klub din Stan Kroenke da sauran daraktocinsa suna bayan kocin.

Wenger zai halarci taron wata-wata na hukumar gudanarwar kungiyar ranar Alhamis din nan kuma maganar ci gaba da zamansa a klub din ba ta daga cikin abubuwan da za a tattauna a taron.

Duk wani batu da ya shafi kociyan wanda kwantiraginsa zai kare a 2014 ya dogara ne a kansa kuma kungiyar a shirye ta ke ta sabunta masa kwantiragin wanda ya fara a 1996 in har yana so.

'Yan hukumar gudanarwar sun fahimci irin mawuyacin halin da kungiyar ke ciki da damuwar magoya bayanta kan rashin daukar kofi amma ba sa nuna wa illa dai sun dukufa wajen samar da abubuwan da ake bukata na bunkasa klub din ta yadda zai yi gogayya da manyan kungiyoyin Turai.

Shugabannin Arsenal din na da kwarin guiwa cewa suna da kudin da zasu iya jawo kwararrun 'yan wasa ko da kungiyar ba ta samu damar shiga gasar Kofin Zakarun Turai ta kaka mai zuwa ba ko da ike dai sun san cewa hakan abu ne mai wuyar gaske.