Man United ta yi galaba a kan QPR

Image caption Ryan Giggs

Ryan Giggs ya zura kwallonsa ta 999 a wasan da Manchester United ta doke QPR.

Giggs ne ya zura kwallo ta biyu da ya ba Man United nasara a kan QPR da ci biyu da nema.

Tun kafin a tafi hutun rabin lokaci ne dai Rafeal ya zura kwallon farko.

A yanzu haka dai Manchester United na gaban Manchester City ne da maki 15.