Ribar Arsenal ta yi kasa warwas

'yan wasan arsenal
Image caption Ribar saye da sayar da 'yan wasa ta yi kasa a Arsenal

Ribar da Arsenal ta ke samu ta ragu matuka zuwa fam miliyan 17.8 cikin watanni shida zuwa watan Nuwamba duk da sayar da Robin van Persie da ta yi a kan fam miliyan 24.

Kungiyar ta samu ribar fam miliyan hamsin ne a bara a daidai wannan lokaci.

Ribar da ta samu daga cinikin 'yan wasa ta yi kasa daga fam miliyan 46.1 a bara zuwa fam miliyan 23.2

Duk da raguwar ribar kudaden ajiyar klub sun karu zuwa fam miliyan 123 daga fam miliyan 115.

Magoya bayan kungiyar na neman ta sayi sababbin 'yan wasa yayin da ta ke fafutukar tsira cikin kungiyoyi hudu na gaba a Premier.

Shugaban klub din na Arsenal Peter Hill-Wood ya kare dabarun kungiyar.

Hamshakin attajiri ba Amurke Stan Kroenke ne ya mallaki mafi yawan hannun jarin klub din.