Federer ya yi nasara a Dubai

roger federer
Image caption Federer ya yunkuro ya yi nasara

Zakaran wasan tennis na biyu a duniya Roger Federer ya tsallake zuwa zagaye na gaba a gasar Dubai Duty Free da nasara a kan Malek Jaziri.

A turmi uku na karawar Jaziri dan Tunisia wanda shi ne na 128 a jerin gwanayen tennis na duniya ya faara galaba a kan Federer.

Sai dai kuma a turmi na biyu da na uku Federer ya yunkuro ya doke Jazirin a wasan da maki 5-7 6-0 6-2.

Sun kammala wasan ne a cikin sa'a daya da minti 30.

Karin bayani