Djokovic ya yi nasara a Dubai

novak djokovic
Image caption Novak Djokovic ya yi nasara a dukkanin wasanninsa bana

Zakaran wasan tennis na duniya Novak Djokovic ya yi nasarar zuwa zagaye na biyu na gasar Dubai Free Trade.

Djokovic dan kasar Serbia ya samu nasarar ne bayan da ya fitar da Viktor Troicki shi ma dan Serbia da maki 6-1 6-4 a mintuna 67.

Da wannan nasara Novak Djokovic ya ci dukkanin wasanninsa tara da ya yi a shekarar nan.