Kyaftin din Man U na lallaba gwiwarsa

Nemanja Vidic
Image caption Nemanja Vidic yace idan har bai samu wani raunin ba, a cikin watanni biyu ko uku masu zuwa to gwiwarsa za ta warke.

Kyaftin din kulob din Manchester United, Nemanja Vidic na fatan nan ba da dadewa ba zai dinga buga duka wasan kulob din, idan gwiwarsa ta warke.

Vidic ya amince cewa har yanzu yana jinyar gwiwar da ta hana shi buga kowane wasa, banda wasanni 14 da ya buga, tun daga shekarar 2011.

"Wasannin da za mu buga a ranar Laraba da Asabar mai zuwa, kamata ya yi in duba na gani ko zan iya shiga ko kuma a'a." Dan wasan ya shaida wa BBC.

"Bayan kowane wasa ina kara jin karfin jikina, hakan wata alama ce mai kyau." Inji Kyaftin din.

Dan wasan mai shekaru 31 ya yi amanna cewa, zai warke sarai nan da karshen kakar wasanni, kuma yace gwiwar ta kumbura, amma ba ta ciwo, bayan taka ledar da ya yi a kwanan nan.

Dan wasan wanda ya taka wa Manchester United leda sau 256 a gasar premier League, yace wani lokacin gwiwar na ciwo, wani lokaci kuma bata ciwo, idan ya buga wasa.

Karin bayani