Gareth ya taka rawar gani - Villas-Boas

Gareth Bale
Image caption Manajan West Ham, Sam Allardyce shi ma ya yabawa Gareth Bale

Manajan Tottenham, Andre Villas-Baos ya ce Gareth Bale, abin koyi ne ga sauran 'yan wasa, saboda nasarar da ya kai kulob din ga samu, a kan West Ham.

An tashi wasan ne Tottenham na da ci uku, yayin da West Ham kuma ke da ci biyu.

Bale ne dai ya fara zura kwallo a ragar West Ham, kuma shi ne ya zura kwallon da ya baiwa Tottenham nasara gab da tashi a wasan.

"Abin koyi ne ga sauran 'yan wasa." Inji Villas-Boas

Ya kara da cewa " 'Yan wasa kamarsa sun san lokacin da ya dace su dauki mataki na kashin kansu, ya burge mutane."

Manajan ya kuma nuna yadda dan wasan ke nuna kwarewa wajen cin kwallo gab da kammala wasa, inda ya ce ba shi da hurumin zaben dan wasan a matsayin gwarzon dan kwallon wannan shekarar, amma yana ganin ya cancanta.

Karin bayani