Nadal ya yi nasara a Mexico

rafeal nadal
Image caption Rafeal Nadal ya na neman farfadowa

Tshohon zakaran wasan tennis na duniya Rafeal Nadal ya fara yunkurin daukar kofinsa na 38 na gasar filin turbaya (clay-court) da nasara a Mexico.

Tsohon zakaran ya yi galaba ne a kan Diego Sebastian Schwartzman wanda ba ya cikin fitattun gwanaye na duniya da maki 6-2 6-2 a wasansa na zagayen farko a gasarATP ta Acapulco.

Nadal wanda ya dawo fagen wasan kwanannan bayan watanni 7 yana jiyyar ciwon guiwa ya fitar da Schwartzman a mintuna 68 ne kawai a Mexico.

Rafeal wanda sau 11 yana daukar kofin manyan gasannin tennis, yanzu zai fuskanci dan Argentina Martin Alund shi ma da baya cikin jerin gwanayen tennis na duniya.

A farkon watannan ne tsohon zakaran ya yi nasarar daukar kofinsa na gasar ta turbaya na 37 a Sao Paulo ta Brazil.

Tsohon zakaran dan kasar Spaniya da a yanzu ya ke matsayi na biyar a duniya ya na kokarin farfado da wasansa a gasar filin turbayar kafin ya koma wasa a filin dabe (hard court)

Ana saran Nadal zai yi wasa a gasar gwanaye a Monaco a watan Aprilu, sannan kuma zai yi wasa a Madrid da Roma kafin fara gasar French Open a Paris.

Karin bayani