Matar Painstil ta janye kara a kansa

john painstil
Image caption An zargi John Painstil da raunata matarsa

Matar dan wasan kwallon kafar nan na Ghana John Paintsil da wani makwabcinsu sun janye tuhumar da suka shigar wajen 'yan sanda a kan dan wasan game da wani rikicin ma'aurata tsakanin painstil din da matar tasa.

Wani jami'in 'yan sanda a Accra babban birnin Ghana wanda ya sanar da hakan ya ce mutanen biyu sun gabatar da koken ne a makon da ya wuce.

Inda suke zargin dan wasan da laifin yi wa matarsa, Richlove rauni da kuma cin mutuncin makwabcin a gidan dan wasan a Accra ranar Juma'a.

Sai dai jami'in 'yan sandan ya ki ya ce uffan game da yamadidin da ake yi cewa Painstil ya jiwa matar tasa rauni da wuka a idanunta.

'yan sandan sun ki bayyana sunan ko wane ne makwabcin tsohon dan wasan na West Ham da Fulham.

A ranar Talata aka kai dan wasan asibiti saboda larurar gajiya da rashin isasshen ruwa a jiki amma daga baya aka maida shi gida ya ci gaba da murmure wa.

John Painstil wanda ya bugawa Ghana wasa a gasar cin Kofin Afrika a Afrika ta Kudu yanzu ya na wasa ne a kungiyar Hapoel Tel Aviv ta Isreala.