Manajan Chelsea zai bar kulob din

Manajan wucin gadi na kulob din Chelsea, Rafael Benitez
Image caption Rafael Benitez ya zargi kulob din da bashi mukamin wucin gadi, saboda idan bai yi nasara ba su kore shi

Manajan wucingadi na kulob din Chelsea, Rafael Benitez ya ce zai bar kulob din a watan Mayu mai zuwa.

Inda ya bayyana bashi mukamin wucin gadi da kulob din yayi, a matsayin babban kuskure ne.

Benitez ya soki wasu daga cikin masoya kulob din, bayan Middlesbrough ta doke Chelsea da ci biyu da nema, a zagaye na biyar na gasar cin kofin FA.

Ya shaida wa BBC cewa " Chelsea ta bani mukamin manaja na wucin gadi, wanda hakan babban kuskure ne, domin ni manaja ne. "

Ya kara da cewa " Su ma masoya kulob din na taimakawa wajen dagula al'amura. Domin haka kada su damu zan tafi a karshen kakar wasanni."

Hirar da Benitez, wanda tsohon manajan Liverpool ne, ta zo ne bayan wasu magoya bayan kulob din sun nuna adawarsu a gare shi.

Benitez mai shekaru 52 ya yi bakin jini a wajen wasu masoya kulob din, tun bayan da ya karbi jan ragamar kulob din, daga hannun Roberto Di Matteo a watan Nuwamba.

Karin bayani