Uefa ta wanke Drogba

didier drogba
Image caption Didier Drogba na da takaddama da Shenhua

Hukumar kwallon kafa ta Turai, Uefa, ta yanke hukuncin cewa Didier Drogba ya cancanci buga wasan kofin Zakarun Turai.

Hukumar ta ce Drogba zai iya yi wa kungiyar Galatasaray ta Turkiyya wasa a gasar ta Zakarun Turai bayan ta yi watsi da karar da kungiyar Schalke ta Jamus ta shigar gabanta kan cancantarsa.

Dan wasan mai shekaru 34 ya buga wa Galatasaray wasa ne a karawarta da Schalke ranar 20 ga watan Fabrairu na kungiyoyi 16 karawar farko da suka tashi 1-1.

Kungiyar ta Jamus ta yi zargin cewa dan wasan dan kasar Ivory Coast bai yi rijista a kan lokaci da Galatasaray din da har zai samu damar buga wasannin gasar na bayan matakin rukuni rukuni.

A kan hakan Hukumar ta Uefa ta ce lamarin ba haka ya ke ba dan wasan ya yi rijista tun ranar 1 ga watan Fabrairu.

Tafiyar Drogban a matsayin aro na tsawon watanni 18 Galatasaray daga Shanghai Shenhua da aka sanar a watan Janairu har yanzu na cike da takaddama.

Shenhua wadda Drogba ya kulla yarjejeniyar shekaru biyu da rabi da kungiyar a kakar wasannin da ta gabata ta ce lamarin tafiyar tasa ya bata mamaki matuka kuma za ta gabatar da korafinta ga hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA.