Sunderland ta hada guiwa da Asusun Mandela

'yan wasan sunderland
Image caption Sunderland na kokarin yada manufar Mandela

Kungiyar kwallon kafa ta Sunderland ta Ingila ta kulla yarjejeniya da Asusun ayyukan taimako na Nelson Mandela.

A watanni 18 masu zuwa kungiyar ta gasar Premier za ta mara baya wajen ayyukan tara kudaden asusun wanda tsohon shugaban Afrika ta kudun ya kafa.

Za a kaddamar da shirin tara kudaden ne a lokacin wasan da klub din zai yi da Mancheser United ranar 30 ga watan Maris.

Shugaban Asusun na Mandela Achmat Dangor ya ce hadin guiwar zai taimaka wajen yada sakon tsohon shugaban mai yaki da mulkin wariyar launin fata.

Wanda sakon shi ne tabbatar da sasantawa tsakanin jama'a da kuma adalci a duniya.

Karin bayani