Bafana na harin gasar cin kofin duniya

Gordon Igesund
Image caption Bafana Bafana za su kara da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a ranar 23 ga watan Maris

Kociyan Afrika ta Kudu Gordon Igesund ya ce ba zu su yi sakaci ba a lokacin da tawagarsa za ta koma fagen daga a wasan share fagen shiga gasar cin kofin duniya ta 2014.

Bafana Bafana za su kara da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a birnin Cape Town a ranar 23 ga watan Maris.

Kuma suna sane da cewa lallai suna bukatar nasara saboda sune na uku a rukunin A bayan da suka yi kunnen doki da Ethiopia da Botswana bara.

Kociya Igesund ya ce za a samu sauye-sauye a tawagar kasar wacce ta kai wasan dab da na kusa da na karshe a watan da ya gabata a gasar cin kofin kasashen Afrika wanda suka dauki bakunci.

"Ba ma cikin yanayin da ya dace a rukunin," a cewarsa. Mun zubar da maki hudu kuma wasanni hudu ne suka rage mana, a don haka an fara tsere mana.

Ethiopia ce ta daya a rukunin, sai Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, sannan Afrika ta Kudu sai kuma Bostwana a matakin karshe.